Isa ga babban shafi
Niger-Chadi-Nigeria

Sojan hadin guiwa na Nijar da Chadi sun kashe 'yan Boko Haram 38

Dakarun kasar Nijar da na Chadi sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram akalla 38 yayin wata karawa da suka yi a kauyuka biyu dake kan iyakan kasashen biyu. 

Wasu mazauna kauyuka da 'yan kungiyar Boko Haram suka tarwatsa daga kauyukan su.
Wasu mazauna kauyuka da 'yan kungiyar Boko Haram suka tarwatsa daga kauyukan su. REUTERS
Talla

Majiyoyin soji na cewa soja biyu na kasashen suka mutu yayin gumurzu da aka yi yankin garin Toumour.

Bayanai na cewa Sojan hadin guiwa tare da na Nigeria sunyi katari wajen kama makamai masu tarin yawa daga mabuyar ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Ya zuwa yanzu ‘yan kungiyar Boko Haran a wannan yanki sun kashe dubban mutane da tilastawa mutane sama da miliyan biyu da dubu dari hudu barin muhallin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.