Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta ce sabon bidiyon Boko Haram abin dariya ne

Yayin da take maida martani kan sabon bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar a ranar Larabar da ta gabata, wanda a ciki ta yi barazanar kama shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, rundunar Sojin Najeriya ta bayyan bidiyon a matsayin abin dariya.

Mai magana da yawun rundunar ojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar
Mai magana da yawun rundunar ojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar via twitter
Talla

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce kungiyar ta Boko Haram tsohon bidiyon ta fitar tun na shekarar 2014, aka kuma yi amfani da fasahar hada hoto wajen makala ‘ya’yan kungiyar da suka rage a yanzu cikin hoton bidiyon.

Mukaddashin Daraktan yada labaran rundunar Sojin Najeriya Brigediya Janar Rabe Abubakar, ya ce bidiyon ya nuna yadda kungiyar ta Boko Haram ta kusan zuwa karshe.

Rabe Abubakar ya kara da cewa, sabon bidiyon bai nuna gaskiyar yawan mayakan na Boko Haram da suka rage ba, tare da bayyana hakan a matsayin farfaganda.

Ya kuma yi kira ga mayakan da su ajiye makamansu don rungumar zaman lafiya, don a cewarsa rundunar sojin Najeriya ba za ta gajiya da aniyarta ta murkushe mayakan ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.