Isa ga babban shafi
Najeriya

Chibok: Sojin Najeriya za su ci gaba da yakar Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya ta ce daukar matakin musayar fursononi Boko Haram domin karbo Matan Chibok ba huruminta ba ne illa gwamnati ce za ta yanke shawara kan matakin.

Janar Abayomi Gabriel Olonisakin
Janar Abayomi Gabriel Olonisakin thenation
Talla

Rundunar Sojin ta mayar da martani ne kan hoton bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar da ke nuna wasu daga cikin ‘Yan Matan da suka sace a Chibok.

Babban hafsan sojin Najeriya Obayomi Olonisakin ya shaidawa manema labarai cewa za su ci gaba da yaki da Boko Haram bayan mayakan sun bukaci a saki fursunoninsu  a madadin ‘Yan matan na Chibok.

Bidiyon da Boko Haram ta fitar ya nuna ‘Yan Mata 50, kuma kungiyar ta ce za ta saki ‘Yan matan idan an saki mayakanta.

Ministan Watsa labarai da al’adu Lai Muhammed ya ce gwamnatin Tarayya tana kan tattaunawa da Boko Haram domin kubutar da ‘Yan Matan Chibok.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.