Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta ce sojin Najeriya sun kashe wasu daga cikin ‘yan matan Chibok

Mai Magana a faifan bidiyon Boko Haram ya shawarci iyayen ‘yan matan sakandaren Chibok da kungiyar ta sace dasu matsawa gwamnatin Najeriya sakin mayakanta kafin ta saki sauran ‘yan matan dake hannunta.

Yan matan sakandaren Chibok da wani mukadashin Kungiyar Boko Haram a sabon hoton bidiyo
Yan matan sakandaren Chibok da wani mukadashin Kungiyar Boko Haram a sabon hoton bidiyo AFP
Talla

A sabon faifan bidiyon da kungiyar ta fitar wadda shine karo na 3 tun bayan garkuwa da daliban shekaru 2 da suka gabata, Mai maganan ya yi bayani game da ‘yan matan inda ya ke cewa wasu daga cikinsu suna nan a raye yayin da yace  sojin Najeriya sun kashe wasu daga cikin ‘yan matan sanadiyar hare haren sama da dakarun suka kai akan mayakan, mai maganan ya kara da cewa kungiyar ta aurar da 40 daga cikin ‘yan matan da ta sace.

An kuma ga yadda a cikin hoton bidiyon ne mai maganan ya umarci daya daga cikin ‘yan matan da ta yi kira ga gwamnatin Najeriya don sakin mayakanta.

A shekara 2014 mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga makarantar kwana ta mata dake a garin Chibok a jahar Borno inda suka yi awon gaba da ‘yan matan 276

Kungiyar Boko Haram dai ta kwashi shekaru akalla 6 tana kai hare haren bama bamai akan al’ummar wasu jihohin arewa maso gabashin kasar inda mutane akalla 20,000 suka mutu wasu sama da miliyan biyu kuwa suka rasa matsuguninsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.