Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na nazarin Bidiyon ‘Yan matan Chibok

Gwamnatin Najeriya tace tana nazari akan wani faifan bidiyon Boko Haram da ya nuna wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok da mayakan suka sace tsawon shekaru biyu da suka gabata.

Boko haram ta nuna 'Yan Matan Chibok 15 daga cikin sama da 200 da ta sace tsawon shekaru biyu
Boko haram ta nuna 'Yan Matan Chibok 15 daga cikin sama da 200 da ta sace tsawon shekaru biyu via CNN
Talla

Hoton Bidiyon dai ya kasance na farko da aka nuna ‘Yan matan na Chibok da aka sace a ranar 14 ga watan Afrilu tun wani bidiyo da ya nuna matan suna karatun Al Qur’ani a watan Mayun 2014 wanda kuma ya nuna Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau yana ikirarin musuluntar da wasu daga cikinsu tare da aurar da wasu

Wata babban majiyar gwamnati ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa suna nazari akan bidiyon wanda ya nuna ‘Yan mata 15 suna zayyana sunayensu.

Majiyar tace a watan Yulin bara jami’an tsaron Najeriya samu irin bidiyon da kafar CNN ta samu.

Gwamnati ta yi kokarin bin diddigi ba tare da samun nasara ba kuma ‘Yan Boko Haram sun nemi a biya su kudi sama da dala miliyan guda domin sakin ‘Yan Mata 10 a cewar majiyar.

Amma majiyar tace gwamnati za ta bi matakan da suka dace tare da yin takatsantsan domin kaucewa irin matsalolin da gwamnatin baya ta fuskanta.

Kafar CNN tace wani mai shiga tsakanin gwamnati da yan Boko Haram ne ya aiko da bidiyon tun a watan Disemba.

Fito da bidiyon dai ya dan sanyaya ran iyayen ‘yan matan na Chibok wanda ke tabbatar da wasunsu suna raye bayan shafe shekaru biyu suna hannun ‘Yan Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.