Isa ga babban shafi
Boko Haram

Boko Haram ta fitar da bidiyon ‘Yan Matan Chibok

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani bidiyo da ya nuna wasu ‘Yan mata 15 daga cikin ‘Yan Makarantar garin Chibok sama da 200 da suka sace yau tsawon shekaru biyu.Gidan Telebijin na CNN ne ya samu faifan bidiyon na ‘Yan Matan na Chibok daga hannun wani mai shiga tsakani tsakanin ‘Yan Boko Haram da gwamnatin Najeriya.

Shekaru biyu da sace 'Yan Matan Chibok
Shekaru biyu da sace 'Yan Matan Chibok via CNN
Talla

CNN tace tun a watan Disemba ta samu bidiyon. Kuma tun a lokacin Gwamnatin Najeirya ta samu bidiyon.

Yau shekaru biyu ke nan cur da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace daliban ‘yan matan sakadaren a garin Chibok da ke kudancin jihar Borno.

Hoton bidiyon, ‘ya nuna yan matan 15 sanye da bakar hijabi suna bayyana sunayensu, tare da bayyana cewa suna daga cikin wadanda Boko Haram ta sace a garin na Chibok.

Wannan dai wata alama ce da ke tabbatar da cewa ‘yan matan sunan na a raye shekaru biyu bayan sace su a Chibok.

A bidiyo, an ji ‘yan matan na cewa ana kula da su sosai, tare da bayyana fatar komawa gida domin ci gaba da rayuwa tare da iyayensu.

Kafafen yada labarai a Najeriya sun jiyo wasu daga cikin iyayen ‘yan matan wadanda tashar talabijin ta CNN ta nuna a jiya na cewa tabbas, wadanda aka nunan ‘yanyansu ne da Boko Haram ta sace.

A ranar 14 ga watan afrilun shekara ta 2014 ne dai ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a garin Chibok, inda suka yi awun gaba da ‘yan mata 276, amma daga bisani 57 daga cikinsu suka yi nasarar tserewa daga hannun maharan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.