Isa ga babban shafi
Najeriya

Iyayen Matan Chibok sun roki Buhari

Iyayen ‘Yan Matan da Mayakan Boko Haram suka sace a wata Makarantar garin Chibok a Jihar Borno sama da shekara guda sun roki shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taimaka ya kubutar da ‘yayansu domin su samu kwanciyar hankali a rayuwarsu.

'Iyayen 'Yan Matan Chibok da Mayakan Boko Haram suka sace 'yayansu na cikin damuwa
'Iyayen 'Yan Matan Chibok da Mayakan Boko Haram suka sace 'yayansu na cikin damuwa REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A jiya Laraba ne a Abuja, Shugaba Buhari ya gana da wasu daga cikin iyayen Matan Chibok da kuma tawagar kungiyar BringBackOurGirls da ke neman ganin an ceto ‘yan matan na Chibok.

“Mr President ka yi juyayin uwa ga ‘yayanta da ke fama da Kuka” a cewar daya daga cikin ‘iyayen ‘Yan Matan Chibok da ke rokon Buhari ya karbo ma su ‘yayansu.

Iyayen sun shaidawa shugaba Buhari cewa wasunsu da dama sun mutu saboda hawan jini da tunanin ‘yayansu da aka sace.

00:31

Iyayen Matan Chibok sun shaidawa shugaba Buhari cewa wasunsu da dama sun mutu saboda hawan jini

Iyayen Matan dai na cikin tashin hankali da damuwa a kullum, yayin da wasu ke tunanin an kashe ‘yayansu, wasu kuma har yanzu suna da yakinin yin tozali da su.

Jagorar kungiyar BringBackOurGirls Oby Ezekwesili ta shaidawa Buhari cewa ba za su yadda da adadin kwanakin da aka kwashe ba ‘Yan Matan Chibok na hannun miyagu.

Buhari ya shaidawa iyayen na Matan Chibok da ‘Yan kungiyar da ke neman an ceto ‘Yan Matan cewa gwamnatinsa tana iya kokarinta wajen kawo karshen matsalar Boko Haram a Najeriya.

An shafe sama da shekara guda babu labari game da ‘Yan Matan Makarantar garin Chibok da Mayakan Boko Haram suka sace.

A ranar 14 ga watan Afrilu 2014 ne Mayakan Boko Haram suka sace ‘Yan Matan Chibok a makarantarsu.

A cikin wani rahoto da ta fitar, Kungiyar Kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International tace sama da Mata da ‘Yan Mata 2,000 Mayakan Boko Haram suka sace tun a 2014 hadi da ‘Yan Matan Makarantar garin Chibok 276 da aka yi garkuwa da su.

Kafin rantsar da Buhari, Shugaban na Najeriya ya ce ba zai yi alkawalin kubutar da ‘Yan Matan ba saboda har yanzu ba a san inda ake garkuwa da su ba.

Amma a cikin sanarwar da ya fitar, Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta domin mika ‘Yan matan ga iyayensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.