Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekaru biyu da sace ‘Yan Matan Chibok

Yau Alhamis 14 ga watan Afrilu ake cika shekaru biyu cur da ‘Yan Boko Haram suka abka Makarantar garin Chibok a Jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya suka sace ‘Yan Mata sama da 200.

Iyayen Matan Chibok na cikin damuwa
Iyayen Matan Chibok na cikin damuwa REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da Kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyo da ke nuna wasu daga cikin ‘Yan Matan na Chibok, al'amarin da ke tabbatar da suna raye.

Kungiyoyi da ke fafutikar ganin an kubutar da ‘Yan Matan sun shirya gudanar da gangami domin nuna alhini tare da ci gaba da yin kiran kubutar da su.

Sace ‘yan matan Chibok sama da 200 dai ya ja hankalin al’ummar duniya.

Iyayen Matan na cikin tashin hankali da damuwa a kullum, yayin da wasu ke tunanin an kashe ‘ya'yansu, wasu kuma har yanzu suna da yakinin yin tozali da su.

Wasunsu da dama sun mutu saboda hawan jini da tunanin ‘ya'yansu da aka sace.

Amma hoton bidiyon wasu daga cikin ‘Yan Matan da Boko Haram ta nuna, zai dan kwantar da hankalin iyayen.

Iyayen Matan sun shirya gudanar da addu’o’I a Makarantar Chibok a yau da ake cika shekaru biyu.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta wallafa rahoto da ke cewa sama da mata 2,000 kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya tun farkon 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.