Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya na zargin wasu mutane 3 da alaka da Boko Haram.

Rundunar Sojin Najeriya  ta sanar cewar tana neman wasu mutane uku ruwa ajallo saboda zargin da ake musu na mu'amala da kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya na cigaba da kakkabe raguwar 'yan Boko Haram daga dajin Sambisa
Rundunar sojin Najeriya na cigaba da kakkabe raguwar 'yan Boko Haram daga dajin Sambisa naij.com
Talla

Daraktan yada labaran rundunar Kanar Sani Usman Kukasheka ya bayana mutanen uku da suka hada da Dan Jarida Ahmed Salkida da Ambasada Ahmed U Bolori da kuma Aisha Wakili.

Jami'in yace ana bukatar mutanen uku dan yi musu tambayoyi kan faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar jiya mai dauke da wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka sace da kuma bayyana 'dan jaridar a matsayin wanda gwamnati zata tattauna da shi a madadin su.

A faifan bidiyon mai magana da yawun kungiyar yace 40 daga cikin yan matan sun yi aure kana wasu daga cikin su kuma sun mutu sakamakon harin sama da sojojin Najeriya suka kai musu inda suka nuna gawawakin su a kwance.

Kakakin na Boko Haram yace a shirye suke suyi musayar 'yan matan da mutanen su da ake tsare da su a Lagos da Abuja da Maiduguri dama wasu sassan Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.