Isa ga babban shafi
Boko Haram

Dakarun Afrika sun yi kadan su yake mu-Shekau

A wani sabon sakon bidiyo, Shugaban Mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya sha alwashin murkushe dakarun hadin guiwa na kasashen Kamaru da Chadi da Najeriya da Nijar da ke yaki da su.

Mayakan Boko Haram, tare da shugabansu Abubakar Shekau
Mayakan Boko Haram, tare da shugabansu Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

“Shugabannin Afrika Yanzu da Sojoji 7,500 za ku yake mu, kun yi kadan” a cewar Shekau a cikin sbon sakon bidiyon mai tsawon minti 28.

Dakarun Najeriya dai sun samu taimakon Dakarun Chadi da Kamaru da Nijar domin yakar Boko Haram.

Shekau ya ce dakaru 7,500 sun yi kadan kamata ya yi a kara dakarun zuwa Miliyan 7.

A cikin bidiyon Shekau ya gargadi shugaban Chadi Idris Deby bayan dakarun kasar sun fafata da i Boko Haram a garin Gamgoru.

Shugaban na Boko Haram ya ce sun kaddamar da yaki ne domin shinfida dokar Allah a duniya ba wai Afrika kadai ba.

Sakon bidiyon na Boko Haram na zuwa ne a yayin da Mayakan suka kaddamar da hari a gidan yarin garin Diffa a Jamhuriyyar Nijar bayan sun kai hari a karshen mako inda mutum guda ya mutu tare da jikkata sama da Ashirin.

Kungiyar Kasashen Afirka ta AU ta sanar da shirin bada gudumawar sojoji, ‘yan sanda da kuma fararen hula 8, 700 don yaki da kungiyar Boko haram a Najeriya.

Wannan ya nuna cewar an samu kari kan sojoji 7,500 da aka amince da su a taron kungiyar wadanda za su fito daga kasashen Najeriya da Chadi, Nijar da Janhuriyar Benin.

Ana saran kungiyar ta AU zata bukaci tallafin kudade daga Majalisar Dinkin Duniya da zaran ta gama tattauna da kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Barazanar Boko Haram ne dai ya sa hukumar zaben Najeriya ta dage babban zaben kasar har zuwa karshen watan Maris saboda Jami'an tsaron kasar sun ce ba za su samar da tsaro ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.