Isa ga babban shafi
Nijar-Najeriya

An kashe ‘Yan boko Haram 109 a Nijar

Hukumomin tsaro a Jamhuriyyar Nijar sun ce mayakan Boko Haram sama da 100 ne aka kashe a musayar wutar da suka yi da dakarun kasar bayan sun kai hari a garin Bosso da ke jihar Diffa. Ministan tsaron Nijar Mahamadou Karidjo ya ce ‘Yan Boko Haram 109 aka kashe, amma akwai Sojoji hudu da fararen hula da suka mutu a musayar wutar da aka yi a jiya Juma’a bayan Mayakan Boko Haram sun shigo garin Bosso.

Motocin sulke na Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya
Motocin sulke na Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya AFP PHOTO / STEPHANE YAS
Talla

Wannan ne dai karon farko da Boko Haram ta kaddamar da hari a Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.

Jami’an leken asirin Amurka sun ce Boko Haram ta fara shan wahala saboda taron dangi da dakarun Chadi da Kamaru da Nijar da Najeriya ke yi wa kungiyar.

Sai dai kuma Jami’an leken asirin sun ce Mayakan na Boko Haram babbar barazana ce ga dakarun Najeriya saboda makaman da suka kwasa a garin Baga.

A ranar Litinin ne dai Majalisar Nijar ake sa ran za ta kada kuri’ar amincewa a tura dakaru domin yakar Boko Haram a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.