Isa ga babban shafi
Nijar-Najeriya

Boko Haram ta kai harin Bom a Diffa

Mayakan Boko Haram na Najeriya sun kai harin bom a garin Diffa na Jamhuriyyar Nijar da ke kan iyaka da Najeriya. Rahotanni daga Diffa sun ce harin kunar bakin wake ne Boko Haram ta kai da safiyar yau Lahadi bayan Sojojin Nijar sun yi nasarar murkushe su a garin Bosso a da suka kai hari makon jiya.

Kofar shiga garin Diffa a Nijar
Kofar shiga garin Diffa a Nijar AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Ministan harakokin wajen Nijar Bazoun Muhammed ya shaidawa RFI hausa cewa akalla mace guda ce ta mutu a harin amma kimanin mutane 16 ne suka jikkata.

Amma kamfanin dillacin labaran Reuters ya ruwaito cewa mutane 5 suka mutu a harin da aka kai a kasuwar Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.