Isa ga babban shafi
Masar

Kasashen yammacin duniya sun aika wakilan su zuwa Masar

A kokarinsu na warware rikcin siyasar da ake fama da shi a kasar Masar, a safiyar yau litinin manzannin kasashen yamma da na larabawa, sun gana da manyan jami’an jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi na kasar Masar wanda yanzu haka ke tsare. Kamfanin dillancin labarai na kasar ta Masar ya ce, cikin mutanen da aka gana da su sun hada da mataimakin shugaban kungiyar Kairat El-Shatar wanda ke tsare a gidan yarin Tora da ke kudancin birnin Alkahira, kuma akwai manzannin Amurka, Tarayyar Turai da kuma Hadaddiyar Daualar Larawaba a cikin tawagar da ta gana da shi.A wani bangaren kuma, hukumomi a Masar suka haramta wa wata ‘yar rajin kare hakkin dan Adam din kasar Yamen, Tawakkol Karman shiga kasar, saboda abin da suka kira dalilan tsaro.Hukumomin filin jirgin saman birnin alkahira sun shaida wa kamfanin dillacin labarum Faraansa na AFP cewa, an dakatar da Karman, a lokacin da ta sauka a kasar, aka kuma tisa keyar ta, ta koma a jirgin da kawo ta daga kasar ta Yamen.Dama Karman, da ita ce macen farko balarabiya, da ta taba lashe kautar zaman lafiya ta Nobel, ta yi ta bayyana goyon bayan ta, ga magoya bayan hambararen shugaba Mohamed Morsi, na kungiyar ‘yan uwa Musulmi. 

Magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar, Muhammad Morsi
Magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar, Muhammad Morsi REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.