Isa ga babban shafi
Masar

An umarci masu zanga zangar kasar Masar su koma gida

Hukumomi kasar Masar sun yi alkawarin kare lafiyar magoya baya hambarren shugaban kasar Mohammad Morsi, in suka gaggauta ficewa daga sansamonin da suka yi, suna zanga zangar adawa da juyin mulkin da aka yi wa shugaban, na kungiyar ‘yan uwa Musulmi. Gamayyar kungiyoyi masu kishin Islama a kasar ta Masar, da ke neman a sako hambararren shugaban, sun sa kafa sun yi fatali da kiran da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta musu, na su watse daga sansanonin da suke zamnan dirshan.Kiran na jiya Alhamis ya zo ne bayan da kwamnadojin ‘Yan sandan kasar sun yi taro, inda suka tattauana yadda za su aiwatar da umarnin da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta musu, na tarwatsa masu boren.Duk wadannan matakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin bin hanyoyin diploomasiyya, wajen kawo karshen zub da jinin da ake yi.Tuni manzo kungiyar taraiyyar Turai a yankin Gabas ta tsakiya Bernardino Leon, da Ministan harkokin wajen kasar Jamus Guido Westerwelle suka isa birnin Alkahira, don kira ga dukkan bangarorin su sasanta.Masu lura da yadda lamura ke tafiya a kasar ta Masar na hasashen yuwuwar samun ci gaba da tashe tashen hankula a sassan kasar ta masar a yau Juma’a. 

Des supporters de l'ex-président Morsi lancent des slogans et portent des cercueils symboliques, lors d'une manifestation au Caire, ce mardi 30 juillet 2013.
Des supporters de l'ex-président Morsi lancent des slogans et portent des cercueils symboliques, lors d'une manifestation au Caire, ce mardi 30 juillet 2013. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.