Isa ga babban shafi
Masar

Babban Hafsan sojin Masar ya nemi magoya bayansa su yi zanga-zanga

Janar Abdel Fattah, da ke sanye da bakin gilashi, a yayin da ya ke jawabi a wajen bukin saukar karatun kananan hafsoshin sojan kasar da aka yi a kusa da Birnin Alexandria, ya umarci ‘yan kasar da su fito kan titunan kasar a ranar Juma’a mai zuwa don bashi goyon baya wajen murkushe ta’addanci da tashe tashen hankula.

Abdel Fattah Al Sisi, kwamandan askarawan sojan kasar Masar
Abdel Fattah Al Sisi, kwamandan askarawan sojan kasar Masar
Talla

Ya ce kafin ya kifar da gwamnatin shugaba Morsi, sai da ya gargade shi, ko dai ya yi murabus ko kuma ya gudanar da kuriar jin ra’ayin jama, amma tsohon shugaban ya yi kunnen kashi.
Sai dai wani babban jami’in jama’iyyar ‘yan uwa musulmi mai suna Essam al-Erian ya yi watsi da wannan kiran, inda yace barazana ce kawai, da ba za ta tsorata su ba.
An ci gaba da samun tashe tashen hankula a kasar, tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Morsi a ranar 3 ga wannan watan na Yuli, kuma wannan kiran da Janar Abdel Fattah al-Sisi, ya sa ana ganin za a ci gaba da samun karin fito na fito tsakanin magoya baya, da masu adawa da Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.