Kungiyar kasashen Turai ta nemi a saki hambararren shugaban kasar Masar Morsi
Babbar Jami’ar diflomasiyar kasashen Turai, Catherine Ashton, ta bayyana bacin ran ta na rashin ganawa da hambararen shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi, lokacin da ta ziyarci kasar.
Wallafawa ranar:
Jami’ar ta bukaci hukumomin kasar Masar, da su gaggauta sakin tsohon shugaban, wanda ta ce an shaida mata cewar yana cikin halin koshin lafiya.
Ashton ta bayyana hakan ne bayan ganawa da ta yi da sababbin shugabannin kasar ta Masar da kuma bagaren masu goyon bayan Morsi.
Wannan kira na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da nuna bore ga gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu