Isa ga babban shafi
Masar

‘Yan uwa Musulmi sun yi watsi da sabuwar gwamnatin Masar

Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta yi watsi da sabuwar Gwamnatin da aka kafa, inda magoya bayan Jam’iyyar suka ce su har yanzu shugaban da suka sani shi ne Mohammed Morsi bayan rantsar da sabbin Ministoci.

Sabuwar gwamnatin Masar ta Adly Mansour da ke samun goyon bayan Sojoji da suka hambarar da gwamnatin Demokradiya ta Morsi
Sabuwar gwamnatin Masar ta Adly Mansour da ke samun goyon bayan Sojoji da suka hambarar da gwamnatin Demokradiya ta Morsi AFP PHOTO/HO/EGYPTIAN PRESIDENCY
Talla

A ranar Talata ne sabuwar Gwamnatin Masar ta rantsar da sabbin ministocin guda 35 da ake ganin ‘Yan boko zalla ne.

‘Yan majalisar Ministocin, da suka hada da Firaministan riko Hazem al-Beblawi, sun dauki ratsuwar fara aiki ne a gaban shugaban rikon da rundunar sojan kasar ta nada, Adly Mansour bayan kifar da gwamnatin Morsi.

Abdel Fattah al-Sisi, da ya jagoranci kifar da gwammnatin tsohon shugaba Morsi ya karbi mukamin mataimakin Firaminista, kuma ministan tsaro.

Wani tsohon jakada a kasar Amurka Nabil Fahmy, ya zama ministan harkokin waje, yayin da tsohon ministan cikin gida, a gwamnatin Morsi, Mohammed Ibrahim, zai ci gaba da rike mukamin na shi.

Akwai Ministoci Mata guda uku a sabuwar majalisar, da suka hada da ministan lafiya Maha El-Rabat, kuma daya daga cikin mata minstocin kirista ce, da ke bin darikar Coptic.

Sai dai tuni jama’iyyar ‘yan uwa musulmi, suka sa kafa suka yi fatali da sabuwar majalisa ministocin, suna masu cewa haramtacciya ce.

Kafin rantsar da sabbin Ministocin akwai arangama da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da magoya bayan Morsi. Jami’an tsaron sun ce akwai mutane sama da 400 da suka cafke.

Masana dai suna ganin darewar bangaren ‘Yan uwa Musulmi daga sabuwar gwamnatin shi ne babban kalubalen da ke gaban gwamnatin Adly Mansour.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.