Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta kafa Kawamiti da zai yi gyara ga kundin tsarin mulkin kasar

A yau Lahadi 21 ga Watan 7 na shekarar 2013 ne kwamitin da zai gudanar da sauye-sauye akan kundin tsarin mulkin kasar Masar zai fara gudanar da ayyukansa, tare da samun wakilci daga sassa daban daban, wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da hatsarin Mota a kasar ta Masar yayi sanadin mutuwar akalla mutane 15.

Shugaban rikon kwarya na Masar Adly Mansour da wasu jama'a
Shugaban rikon kwarya na Masar Adly Mansour da wasu jama'a AFP PHOTO/HO/EGYPTIAN PRESIDENCY
Talla

Kwamitin, wanda gwamnatin rikon kwaryar Masar a karkashin jagorancin shugaba wuccin-gadi Adly Mansour ta Kafa a kasar, a jiya Asabar, na dauke da farfesoshin jami’a hudu da kuma manyan alkalai guda shida.

Ana sa ran kwamitin zai yi gyran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar wanda sojoji suka jingine tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Muhammad Morsi inda aka basu kwanaki 30 su kammala ayyukansu.

Babban kwamitin zai kumshi ‘yan Siyasa, da ‘yan kasuwa, da kungiyoyin Addini da kuma Soji, sannan Kwamitin na da tsawon wa’adin wasu Watanni biyu da zai yi aiki domin yin sauyi ga kudin tsarin mulkin kasar kamin gabatar da shi ga shugaban kasa.

Bayan wannan kuma shugaba Mansour na da tsawon Wata daya ma’ana kwanaki Talatin ya kira taron jin ra’ayoyin jama’a akan batun.

A dai cikin watan Disamban shekarar 2012 ne hambararriyar gwamnatin Morsi ta yi chanji wa kundin tasrin mulkin mai cike da sarkakiya tare da samun rinjayen kashi 64 masu goyon baya.

A wani labarin kuma hatsarin Mota da aka samu a kasar ta Masar yau ya hallaka akalla Sojin kasar Goma sha biyar [15] a yayinda ya jikkata wasu 40.

Hatsarin dai ya auku ne a yankin Lardin Nile Delta dake a Beheira, Motar dai na tafiya ne a kan babban Titin El-Alamein zuwa wani wurin daban lokacin da hatsarin ya auku, sai dai Direban Motar ya tsira da Ran sa.
 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.