Amurka
Amurka tace Belmoktar ne ya kai hari a Algeria
Hukumomin shari’a a kasar Amurka, sun bayyana Moktar Belmoktar wanda aka ce shi ne shugaban kungiyar Alqa’ida a yankin Magreb da kuma Sahel, a matsayin wanda ke da hannun wajen kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 38 a wani kamfanin gas da ke kasar Algeria cikin watan janairun wannan shekara.
Wallafawa ranar:
Talla
Amurka dai na zargin shugaban na AQMI ne da hannu wajen aikata laifuka akalla 8 da suka hada da taimakawa Alqa’ida domin aikata ta’addanci da kuma laifin kisan kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu