Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

‘Yan al Qaeda sun ce sun rataye Bafaranshen da suka sace a Mali

Gwamnatin Faransa tana kokarin tabbatar da gaskiyar ikirarin ‘Yan kungiyar Al Qaeda da suka ce sun rataye Bafaranshen da suka yi garkuwa da shi a Mali.

Mayakan Al Qaeda tare da Faransawa biyu da suka yi garkuwa da su a kasar Mali
Mayakan Al Qaeda tare da Faransawa biyu da suka yi garkuwa da su a kasar Mali AFP
Talla

Wani da ya kira kansa kakakin Kungiyar Al Qaeda reshen Maghreb ya shaidawa kamfanin Dillacin labaran kasar Mauritania ANI cewar sun rataye Bafaranshe Philippe Verdon a ranar 10 ga watan Maris domin mayar da martani ga yakin da Faransa ta kaddamar a Mali.

Kakakin kungiyar ya dora alhakin kisan ga shugaban Faransa Francois Hollande tare da gargadin ci gaba da wanzar da hukuncin idan har dakarun Faransa ba su fice a Mali ba.

Ma’aikatar harakokin wajen Faransa tace tana gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar labarin.

Akalla Baransawa 15 ne aka yi garkuwa da su a Nahiyar Afrika hadi da Verdon da aka kashe.

A ranar 24 ga watan Nuwamban bara ne Mayakan Al Qaeda suka sace Verdon tare da Serge Lazarevic a wata Otel da ke birnin Hombori a arewa maso gabacin Mali.

Mayakan Al Qaeda sun zargi Faransawan a matsayin ‘Yan leken asiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.