Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta ci gaba da fada da ayyukan ta'addanci a cewar Hollande

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande wanda ke gabatar da jawabi dangane da cika shekara daya da harin da wani mai suna Mohamed Merah ya kai wa makarantar Yahudawa da ke birnin Toulouse na kudancin kasar, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da fada da ayyukan ta’addanci a duniya.

Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Shugaban kasar Faransa, François Hollande REUTERS/Laurent Dubrule
Talla

Hollande ya ce ta’addanci matsala ce da ta gama duniya, saboda haka akwai bukatar kara daura damara domin tunkarar ta.

Shugaban na Faransa dai ya furta wadannan kalamai ne a gaban wasu mutane da yawansu ya kai akalla dubu daya da dari biyar. Inda kuma ya kara kare dalilan da suka sa Faransar ta aike da sojojinta zuwa kasar Mali domin fada da wannan matsala ta ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.