Isa ga babban shafi
Masar

Mata uku sun mutu a rikicin Masar

An tabbatar da mutuwar mutane uku dukkaninsu mata, a wani artabun da aka yi tsakanin magoya bayan hambararen Shugaban kasar Masar Mohammad Morsi da kuma masu adawa da shi. Rahotanni sun ce an yi kazamin artabu tsakanin bangarorin biyu ne a garin Mansura da ke cikin lardin Nile Delta inda aka yi amfani da wukake da kuma sauran kananan makamai domin kai wa juna hari, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matan uku sannan aka raunata mutane da dama a cewar majiyoyin kiwon lafiya.

Dubban magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi
Dubban magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Rikicin Masar na kara zafafa, sama da mako biyu da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi wanda shi ne shugaban Demokuradiyya na farko da aka zaba a Kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.