Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Machar zai halarci bikin zaman lafiya a Sudan ta Kudu

A ranar Laraba ake saran jagoran ‘yan tawayen Sudan ta Kudu, Riek Machar ya koma babban birnin Juba don halartar taron bikin cimma yarjejeniyar zaman lafiya bayan ya shafe sama da shekaru biyu a kasar waje.

Riek Machar
Riek Machar REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Sama da shekaru biyu kenan da Machar ya fice daga kasar bayan tabarbarewar yarjejeniyar zaman lafiya ta farko.

Ofishinsa ya ce, jagoran ‘yan tawayen zai gudanar da bikin ne a wuri guda da babban abokin hamayyarsa kuma shugaban kasar, Salva Kiir, koda yake bangren gwamnatin kasar bai bayar da tabbaci kan haduwarsu.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne, Machar da ke fuskantar matsin lamba daga Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma wasu kasashen Yamma, ya cimma yarjejeniyar zaman lafiya da bangaren gwamnatin kasar bayan tabarbarewar yarjejeniyoyin farko.

A shekarar 2016 ne Machar ya tsere zuwa Jamhuriyar Demokradiyar Congo mai makwabtaka da Sudan ta Kudu kafin daga bisa ya isa Afrika ta Kudu, in da aka yi masa daurin talala har zuwa lokacin da aka fara wata sabuwar tattauna a watan Juni.

Sudan ta Kudu da ta kasance jinjirar kasa a duniya, ta tsunduma cikin yakin basasa a karshen shekarar 2013, lokacin da dakarun da ke goyon bayan shugaba Kiir suka yi artabu da dakarun da ke goyon bayan Machar.

Jim kadan da barkewar wannan rikici da ake dangantawa da na kabilanci ne, aka samu wasu tashe-tashen hankulan a sassan kasar, abin da ya kai ga rufe tashoshin hakar man fetir, yayin da miliyoyin mutane suka tsere daga kasar baya ga dubbai da suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.