Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

An kulla yarjejeniyar karshe tsakanin Kiir da Machar

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da abokin hamayyar siyasarsa, Rieck Machar, sun sanya hannu kan yarjejeniyar karshe domin raba madafan-iko a tsakaninsu da nufin kawo karshen rikicin kasar.

Salva Kiir da Riek Machar na musafaha da juna
Salva Kiir da Riek Machar na musafaha da juna SUMY SADURNI / AFP
Talla

Mutanen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar ce a birnin Khartum na Sudan da ke makwabtaka da kasar a ranar Lahadi, kuma abu na farko da yarjejeniyar ke nufi shi ne, Machar na da damar sake komawa kasar a lokacin da yake bukata.

Wani abu da yarjejeniyar ta kunsa shi ne, raba madafan-iko a tsakaninsu domin kafa gwamnatin hadaka, in da ake fatan mutanen biyu da ke hamayya da juna za su yi aiki tare da kuma kokarin dawo da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

An gudanar da bikin cimma yarjejeniyar ce a gaban manyan baki da suka hada da shugaban Sudan, Umar Hassan Albashir da takwarorinsa na Kenya da Uganda da kuma Djibouti.

Bayan kulla yarjejeniyar, bangarorin na da watanni uku a gaba domin kafa gwamnati mai ministoci 35, wadda za ta tafiyar da lamurran kasar har tsawon shekaru uku, Salva Kiir zai samu ministoci 20, yayin da Rieck Machar zai samu 9, sai kuma sauran mukaman da za a raba tsakanin jam’iyyun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.