Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Cibiyoyin Demokradiya sun kintsa wa zaben Zimbabwe

Cibiyoyin Kare Demokradiya a duniya, IRI da NDI sun bayyana shirinsu na tura wata tawagar hadin gwiwa da za ta sanya ido a zaben shugabancin kasar Zimbabwe da za a gudanar a cikin watan Juli mai zuwa.

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

A yayin da shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ke maraba da masu sanya ido na kasashen duniya a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 30 ga watan Juli, Cibiyoyin Kare Demokradiya na IRI da NDI da ke da ofishi a Amurka sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa da ke bayyana shirinu na aikewa da wata tawaga ta musamman don sanya ido a zaben.

Tuni wannan tawaga da aka ba ta suna ZIEOM, wato Zimbabwe International Election Observation Mission ta bude ofishi a Milton Park, wani bangrae a babban birnin Harare, in da ta fara aiwatar da shirye-shiryen aikin sa idon.

Kazalika daga ranar 2 zuwa 9 ga watan Juni ne, wasu manyan jami’an tawagar za su isa Zimbabwe don tantance irin kintswar da gwamnatin kasar ta yi game da gudanar da sahihin zabe, yayin da kuma ake saran za su bada shawarwari kan yadda za a karfafa gwiwar al’umma don shiga a dama da su a zaben.

Sannan a ranar zaben, tawagar ta ZIEOM za ta wakilta jami’anta a sassa daban daban na kasar, in da kuma za su yi aiki tare da wasu masu sanya idon da suka hada da kungiyoyin cikin gida.

Cibiyoyin IRI da NDI sun gudanar da ayyukan sanya ido fiye da 200 a zabukan kasashen duniya, lamarin da ya sa ake ma su kallon kwarewa da kuma kauce wa daukan bangaranci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.