Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Ma'aikatan Zimbabwe sun yi watsi da karin kashi 10 kan albashinsu

Kungiyoyin ma’aikata a kasar Zimbabwe sun yi watsi da tayin da gwamnatin Emmerson Mnangagwa ta yi musu na karin kaso 10 cikin dari kan albashinsu, bayan da tun farko suna mika bukatar kara musu albashin zuwa ninkin dari bisa dari.

Manyan ma’aikata a Zimbabwe dai na daukar akalla dala 591 yayinda kananan kuma ke daukar dala 253 kowanne wata.
Manyan ma’aikata a Zimbabwe dai na daukar akalla dala 591 yayinda kananan kuma ke daukar dala 253 kowanne wata. DESMOND KWANDE / AFP
Talla

A makon jiya ne dai shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya amince da karin kasha 10 na albashin ga jami’an soji da ‘yansanda da sauran kananan ma’aikata kafin nan da watan Yuli lokacin da kasar za ta gudanar da zabenta karon farko tun bayan hambarar da gwamnatin Robert Mugabe.

Sai dai kuma a cewar wata kungiya ta musamman da ke wakiltar ilahirin ma’aikatan kasar har yanzu karin na kaso 10 cikin dari bai taimaka ta yadda dubban ma’aikatan za su fice daga kangin talauci ba.

Manyan ma’aikata a Zimbabwe dai na daukar akalla dala 591 yayinda kananan kuma ke daukar dala 253 kowanne wata.

Zimbabwe dai na kasha akalla kasha 90 cikin dari na kowanne kasafin kudinta wajen biyan albashi da kudaden Fansho, sai dai kuma Emmerson Mnangagwa na fatan daidaita matsalar kafin babban zaben kasar wanda ba a sanar da ranar da za a gudanar da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.