Isa ga babban shafi
Zimbabwe

EU za ta sanya ido kan Zaben Zimbabwe

Kungiyar Kasashen Tuari ta ce, a karon farko za ta sanya ido kan zaben shugaban kasar Zimbabwe da za a yi a watan Yuli mai zuwa, shekaru 16 bayan ta yi hannun riga da tsohon shugaban kasa Robert Mugabe.

Zimbabwe za ta gudanar da zaben shugaban kasa bayan kawar da tsohon shugabanta Robert Mugabe daga karagar mulki a bara
Zimbabwe za ta gudanar da zaben shugaban kasa bayan kawar da tsohon shugabanta Robert Mugabe daga karagar mulki a bara
Talla

Wakilan kungiyar da na gwamnatin Zimbabwe sun sanya hannu kan yarjejeniyar aiki tare a birnin Harare, bayan gwamnatin ta gayyace su.

Philippe van Damme, shugaban tawagar kungiyar ya yaba wa gwamnatin kasar kan matakan da take dauka, yayin da Ministan Harkokin Waje, Sibusiso Moyo ya ce a bude kofar kasar ta ke ga kasashen duniya domin ganewa idan su halin da ake ciki.

Zaben zai kasance shi ne na farko tun bayan kawar da Mugabe daga karagar mulki a cikin watan Nuwamban da ya gabata, lokacin da sojojin kasar suka yi masa tawaye har suka karbe ikon tafiyar da kasar daga hannunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.