An bayyana ranar gudanar da zabubuka a kasar Zimbabwe
Mujallar wallafa labarai da kudurorin gwamnati, ta ce shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ne ya amince da ranar ta 30 ga watan yuli domin gudanar da zaben shugaban kasa, na ‘yan majalisa da kuma na kansiloli.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan dai zai kasance karo na farko da za a gudanar da zabubuka a kasar ta Zimbabwe ta bayan kawar da Robert Mugabe daga madafun iko.
Tuni Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana aniyarta ta tallafa wa kasar domin samun nasarar gudanar da wadannan zabubuka, da suka hada da samar da kudade da kuma kwararri domin shirya zaben a cikin kyakkyawan tsari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu