Kotu a Kenya ta umurci gwamnati ta bude gidajen Talabijin da ta rufe
Kotu a Kenya ta bayar da umurnin bude wasu gidajen talabijin da gwamnatin kasar ta rufe saboda nuna bikin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa da jagoran ‘yan adawa Raila Odinga ya yi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kotun ta bayar da umurnin sake bude tashoshin ne kafin ta yanke hukuncin karshe a kai a cikin kwanaki 14 masu zuwa.
To sai dai kungiyoyin kare hakkin fadin albarkacin baki, na ganin cewa bai kamata a rufe wadannan gidajen talabijin ba, domin kuwa sun yi aikinsu ne na yada labarai.
Gidajen talabijin da aka rufe sun hada da NTV, Citizen TV da kuma KTN News.
A ranan larabar da ta gabata, Ministan cikin gida ya shaida cewar gidajen talabijin din zasu ci gaba da kasance wa a rufe har sai an kammala binciken da ake gudanar wa akansu.
Shima dai Ministan tsaron kasar Fred Matiang’i, ya zargi wasu kafafen yada labarai wajen taimakawa da ingiza rikici a kasar abinda kan iya janyo dubban mutane cikin hadari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu