Isa ga babban shafi
Kenya

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Kenyatta

Kotun kolin kasar Kenya ta yi watsi da korafe-korafen da aka shigar gabanta kan soke maimaicin zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar 26 ga watan Oktoba, tare da amincewa da sahihancin nasarar Uhuru Kenyatta.

Uhuru Kenyatta
Uhuru Kenyatta REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Kotu ta ce korafin da aka shigar gabanta ba shi da wani tushe, don haka ta tabbatar da sahihancin zaben da ya bai wa Uhuru Kenyatta nasara a koro na biyu.

Hukuncin da alkalin kotun, Justice David Maraga, ya bayar zai bada daman rantsar da Kenyatta ranar 28 ga watan Nuwamba da muke ciki, tare da kawo karshan rudanin da siyasar kasar ta fuskanta.

A watan Satumba da ya gabata Alkali Maraga ya soke zaben farko da aka gudanar ranar 8 ga watan Agusta kan hujojjin kura-kurai da aka tabbatar an samu waje gudanar da zaben.

Hukuncin shi ne irinsa na farko a tarihi da aka taba gani a nahiyar Afirka, wanda kuma ya sake harzuka rikici musamman zanga-zangar da magoya bayan Raila Odinga da ya kauracewa zaben a karo na biyu ke yi.

Kenyatta dai ya samu kuri’u 98 cikin 100 a maimaicin zaben na watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.