Isa ga babban shafi
Afrika

Ana ci gaba da fuskantar rashin tsaro a Afrika ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akalla mutane 10 ne suka mutu cikin makon nan bayan barkewar rikici tsakanin bangarori biyu masu adawa da juna da ke rike da makamai a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

Tawagar Sakataren MDD Antonio Guterres a Afrika ta Tsakiya
Tawagar Sakataren MDD Antonio Guterres a Afrika ta Tsakiya RFI/Pierre Pinto
Talla

Wani fada ya kaure tsakanin kungiyoyin mayakan Seleka Musulmi da kuma mayakan Balaka mabiya addinin Kirista.

Daya daga cikin shugabanin ya sheidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a Larabar da ta gabata kadai, sun binne mutane 10 da suka hada da mayakan da kuma fararen hula, inda kuma ya ce matukar aka ci gaba da hakan ba tare da daukar mataki ba zuwa yau adadin kan iya haura mutune 40.

Jamhuriyyar Afrika ta stakiya da ke cikin kasashe da ke fuskantar koma baya da talauci a duniya yanzu haka na kokarin farfadowa ne daga yakin basasar da ta tsunduma a shekarar 2013 bayan hambarar da mulkin shugaba Francoise Bozize.

Majalisar dinkin duniya ta ce rikicin kasar ya hallaka mutane da dama tareda tilastawa sama da mutum dubu dari biyar barin gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.