Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakkiya

Kwana guda da barin Fafaroma Bangui an kashe Musulmi guda

Rahotanni daga Janhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ce an kashe wani Musulmi kwana guda bayan ziyarar da Paparoma Francis ya kai unguwar da al’ummar Musulmin Bangui suke.

Shugaban darikar Katholika Fafaroma Francais a Bangui na Afrika ta Tsakiya
Shugaban darikar Katholika Fafaroma Francais a Bangui na Afrika ta Tsakiya REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Ibrahim Hassan Frede, mai magana da yawun kungiyoyin Musulmin kasar, ya ce yau da safe wani Musulmin da yake so ya fice daga unguwar da suke ya gamu da wasu matasan anti balaka wadanda suka kashe shi nan take.

Frede yace sun dauko gawar mamacin dan yi mata jana’iza a Masallachin unguwar.

Paparoma Francis ya bukaci al’ummar kasar su aje makaman su, su kuma yafewa juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.