Rikici ya dagula zaben raba gardama a Bangui
Akalla mutane biyu suka mutu a rikicin da ya barke a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya a yayin da ake gudanar da zaben raba gardama kan sabunta kundin tsarin mulki.
Wallafawa ranar:
Rikicin ya barke ne a yankunan Musulmi a Bangui tsakanin masu sabanin ra’ayi akan sabon kundin tsarin mulkin.
Sannan an yi harbe-harbe da manyan bindigogi tare da harba makamin roka a wata Makaranta da mutane ke jiran su kada kuri’a.
Zaben dai ya kasance zakaran gwajin dafi ga zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisu da za a gudanar a ranar 27 ga watan Disemba.
Sabon kundin tsarin mulkin da ‘Yan kasar za su amince ya kunshi takaita wa’adin shugabancin kasar zuwa wa’adi biyu, tare da kaddamar da yaki da cin hanci da rage karfin kungiyoyin kasar masu dauke da makamai.
An shafe shekaru biyu Afrika ta tsakiya na cikin rikici mai nasaba da addini tsakanin Mayakan Seleka musulmi da kuma anti-Balaka kiristoci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu