Tarzoma ta barke a Afrika ta tsakiya kan takarar shugabanci Bozize
Sabuwar tarzoma ta kunno kai a birnin Bangui na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, inda masu zanga-zanga suka kafa shingaye a tsakiyar hanya.Rikicin ya biyo bayan umarni da kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta yanke na haramtawa tsohon shugaban kasar Francois Bozize tsaya wa takarar a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 27 ga watan Disamba shekarar nan.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce anyi ta jin karar harbe-harben bindiga a yankuna takwas na birnin yayin da kasar Faransa ta bukaci al-ummarta da su kaurace wa yankunan.
A na dai kyautata zaton cewa zaben zai dawo da kwanciyar hakankali a kasar wadda ta shafe shekaru biyu tana fuskantar rikici tsakanin Musulmai da Krista.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu