Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Bozize ya nisanta kansa da rikicin Afrika ta tsakiya

A daidai lokacin da sabon fada ya barke a birnin Bangui na Jamhuriyar tsakiyar Afirka, Tsohon shugaban kasar da ke gudun hijira a Faransa Francois Bozize, ya nisanta kansa da rikicin wanda Sojojin Seleka suka hambarar.

François Bozizé, Tsohon shugaban Afrika ta tsakiya
François Bozizé, Tsohon shugaban Afrika ta tsakiya - Africanarguments.org
Talla

Bozize ya yi kira zuwa ga kwantar da hankula, tare da yin watsi da zargin yana mara wa Kiristoci baya da ke rikici da musulmi a kasar.

Bozize ya shaidawa RFI cewa ba za a iya samun zaman lafiya ba matukar Michel Djotodia ne shugaban kasa.

Michel Djotodia, Shugaba Musulmi na farko a Tsakiyar Afrika kuma wanda ya jagoranci mayakan Seleka da suka tumbuke Bozize ya zargi tsohon shugaban akan yana goyon bayan Kungiyoyin sa-kai na Kiristoci.

Ya zuwa yanzu alkallumma sun ce daruruwan mutane ne suka mutu tun barkewar rikicin na addini a kasar Tsakiyar Afrika wanda ya sa wasu dubban mutanen kasar suka kauracewa gidajensu.

Bozize ya yi kira ga Djotodia ya yi murabus domin kawo karshen rikicin kasar. Amma shugaban Faransa Francois Hollande, wanda ya aika da dakaru 1,600 domin wanzar da zaman lafiya ya bukaci a gudanar da zaben shugaban kasa cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.