Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Sabon rikici ya balle a Africa ta Tsakiya

Wasu mayakan sa kai Kiristoci dauke da muggan Makamai, sun kai hari a sansanin Sojin kasar Jamhuriyar Afruka ta tsakiya da ke Birnin Bangui. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Dakarun kasar Faransa da na kasashen Afrika ke fafutukar shawo kan tashin hankalin Kabilanci da ya barke a kasar.Harin dai ya wakana ne a wajen birnin na Bangui, yankin Arewaci kamar yanda wani Janar din Sojan kasar, mai suna Mahamat Tahir Zaroga ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.Ance wannan harin shi ne na biyu da aka tabbatar da cewar mayakan sa kai na kungiyar Anti-Balaka ta Kiritocin kasar suka kai, sai dai ba’a bada labarin rasa Rayuka ba.Rugugin harbe-harben bindigogi dai ya barke a tsakkiyar dare a birnin Bangui, inda aka jibge Dakarun Sojin Faransa har 1,600 da na kasashen Afrika 4000, domin shawo kan bazuwar tashin hanakalin, da ke da nasaba da Addini.Shaidun gani da Ido da suka kasance makale a cikin Gidajensu, sun tabbatar da aukuwar musayar wuta da Bindogogi masu karfin gaske a tsakkiyar Ben Zvi mai makwabtaka da Bangiu, kamin faduwar Rana, daga bisani kuma al’amurra suka rinchabe da tsakar Dare.An dai kafa wannan Kungiyar ‘yan ta’addan Anti-Balaka ne domin maida martani ga ‘yan tawayen Seleka da suka taimakawa Michel Djitodia ya karbe madafun ikon kasar, a matsayin shugaban farko Musulmi, a kasar da akasarin al’ummar ta Kiristoci ne, sakamakon juyin mulkin watan da aka yi a watan Maris na shekarar 2013Kusan mutane Dubu 100 ne suka tserewa matsugunnan su, kuma hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kashedin cewar mai yuwa ne a fuskancin tursasawa kananan yara, sakamakon halin yakin da kasar ta samu kanta a ciki.Hukumar ta yi kashedin ne saboda cigaba da saka Kananan yara shiga ayyukan Soji da ake yi, kamar yanda Jami’in UNICEF a kasar Souleymasne Diabate ke cewa. 

Wasu 'yan gudun hijirar Africa ta Tsakiya
Wasu 'yan gudun hijirar Africa ta Tsakiya REUTERS/Andreea Campeanu
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.