Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Faransa ta nemi a dauki matakan gaggawa a Tsakiyar Afrika

Faransa ta nemi kashen duniya su dauki matakan gaggawa a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya saboda tashe tashen hankulan da ke faruwa a kasar. Wannan kiran kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke nazarin aika wasu dubban dakaru a tsakiyar Afrika.

Bindigogi mallakar dakarun Sojin Seleka na Jamhuriyyar tsakiyar Afrika
Bindigogi mallakar dakarun Sojin Seleka na Jamhuriyyar tsakiyar Afrika Laurent Correau / RFI
Talla

Shugaba Francois Hollande ya bayyana wa ministocin shi cewa kasahsen duniya ba za su amince da cin zarafin jama’a da ake yi a kasar Africa ta tsakiya ba.

Faransa ta bayyana fargaba ne musamman ta la’akari da alkalumman da suka nuna an samu mutuwar yara kanana da 25, kuma mutane Miliyan daya da rabi ne ke cikin matsanancin halin rashin abinci da hare haren ‘Yan bindiga.

A farkon watan Disemba ne ake sa ran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’ar amincewa da kudirin daukar mataki a tsakiyar Afrika, lamarin da zai ba dakarun Faransa da na Afrika damar shiga kasar.

Tun lokacin Michel Djotodia ya hambarar da gwamnatin Francois Bozize a watan Maris ragowar ‘yan tawayen Seleka da ya jagoranta a baya, suka ci gaba da gallaza wa jama’a a kasar.

Djotodia ne musulmin farko da ya jagoranci kasar da Faransa ta yi wa Mulkin mallaka, amma akasarin al’ummarta Kiristoci ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.