Dubban mutane na tserewa daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Dubban mutane ne suka tsere daga yankunan da sabon rikici ya barke tsakanin tsoffin ‘yan tawaye da mayakan sa kai a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, lamarin da ya sa ake fargabar barkewar rikicin addini a kasar.
Wallafawa ranar:
Kasar ta shiga rudani tun bayan da mayakan na Seleke suka karbe ikon babban birnin Bangui suka kuma jingine gwamnatin Francois Bozize a watan Maris.
Shugaban ‘yan tawayen Michel Djotodia ya nada kansa a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar tare da rushe hadakar kungiyoyin ‘yan tawaye da suka gaza wajen kare rikici tskanin mayakan sa kai.
Sabon rikicin ya barke ne a kudancin garin Bouca kilomita 290 daga arewacin birnin Bangui.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu