Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Za a kai karin sojoji zuwa Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

An fara kai karin sojojin da za su taimaka wa dakarun samar da zaman lafiya na nahiyar Africa, zuwa Jamahuriyar Afrika ta tsakiya. Sai dai wata majiya na cewa sojojin, da yawan su ya kai 3,600, ba za su kammala isa kasar ba, kafin shekarar 2014.Tun bayan da ‘yan tawaye suka kifar da gwamnatin Francois Bozize a watan Maris din wannan shekarar, kasar mai arzikin ma’adinan da suka hada da zinare, lu’u’lu’u da uranium, ta fada cikin tashe tashen hankula.Jami’an MDD sun bayyana cewa dukkakn bangarorin da ke rikici da juna suna aikata laifukan yaki a yayain tashe tashen hankulan.Kasar Faransa, da ita ta yi wa jamahuriyar Afrika ta tsakiya mulkin mallaka, ta nemi kashen duniya su dauki matakan hana mata bin shiga sawun Somaliya, da ke fama da yake yake tsawon shekaru.Yanzu dai za a kara kai wasu sojojin, da za su tallafa wa 1100 na nahiyar Afrika, da ke aiki a can.Wani jami’in da ya halarci taron da ake yi a kasar Gabon yace, a wannan watan na satumba sojojin za su cika 2000, yayin da ake sa ran su kai 3600 a watan junairun shekara mai zuwa.A watan da ya gabata aka rantsar da, Michel Djotodia, da ya karbe mulki yayin da ‘yan tawayen kasar ke bore, a matsayin shugaban kasar, sai dai har yanzu ya gagara hana ‘yan bindiga kisan mutane da kwasar ganima. 

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Michel Djotodia
Shugaban Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Michel Djotodia
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.