Isa ga babban shafi
Chadi-Afrika ta Tsakiya

Mutanen Chadi sun fara ficewa Bangui

Yanzu haka dubban ‘yan asalin kasar Chadi ne ke ci gaba da ficewa birnin Bangui da kuma wasu yankuna Jamhuriyar Afirka ta tsakiyar domin kaucewa daukar fansa a kansu, bayan da aka zargi sojojin kasar da kashe fararen hula masu zanga-zanga.

Sansanin 'Yan gudun hijira da ke ficewa Bangui kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika
Sansanin 'Yan gudun hijira da ke ficewa Bangui kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Mai shari’a Ousman Mamadou Affono yace tuni bangaren shari’a na kasar ta Chadi ya fara gudanar da bincike dangane da zargin kashe jama’ar kasar da kuma kwace masu dukiyoyi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Yawancin mutanen Chadi dai Musulmi ne kuma akan haka ne wasu mutanen Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya suka shiga farautarsu domin daukar fansa.

Irin haka ne kasar Sudan tace zata bi sahun Chadi domin kwashe ‘yan kasarta a Jamhuriyyar tsakiyar Afrika.

Dakarun Sojin Chadi dai suna cikin Sojojin Afrika da Faransa da suka je kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya domin aikin wanzar da zaman lafiya a kasar bayan ballewar rikici tun lokacin da mayakan Seleka suka kifar da gwamnatin François Bozize inda yanzu Michel Djotodia ne shugaban kasa kuma musulmi.

Alkalumma sun ce sama da mutane 1,000 ne aka kashe a rikicin na kabilanci da aka kwashe makwanni ana yi a Bangui.

Ana zargin dakarun Chadi ne akan suna goyon bayan mayakan Seleka musulmi bayan da suka budewa masu zanga-zanga wuta.

Yanzu haka akwai ziyarar kwanaki uku da Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian zai kai a Mali da Chadi da Nijar domin tattauna rikicin Jamhuriyyar tsakiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.