Ana zaben raba gardama a Afrika ta tsakiya
Al’ummar kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya mai fama da rikici na jefa kuri’ar zaben raba gardama a yau Lahadi kan sabon kundin tsarin mulki wanda ake ganin tamkar zakaran gwajin dafi ga samar da zaman lafiya a kasar.
Wallafawa ranar:
Zaben na zuwa ne duka makwanni biyu da Fafaroma Francis ya kai ziyara a Bangui inda ya yi kira ga al’ummar Musulmi da Kirista a kasar su zauna lafiya a matsayin ‘yan uwan juna.
Rikici dai ya hana aiwatar da cikkakken tsarin gudanar da zaben.
Kuma yanzu haka kalilan ne ke da masaniya ga abinda sabon kundin tsarin mulkin ya kunsa domin kwafi 15,000 aka buga kamin soma zaben.
Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne a 2013 bayan ‘Yan tawayen Seleka yawancinsu Musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize. Daga lokacin ne kuma rikicin kasar ya rikide ya koma na addini tsakanin Seleka da anti-balaka Kiristoci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu