Isa ga babban shafi
Afrika

'Yan tawaye sun kashe mutane a Afrika ta Tsakiya

Wasu mutane dauke da makamai sun kashe fararan hula takwas a sansanin ‘yan gudun hijra da ke jamhuriyar Afrika ta tsakiya, kwanaki kalilan bayan ziyarar da shugaban darikar katolika ta duniya Paparoma Francis ya kai kasar.

'Yan tawayen Anti-Balaka da ke fada da na Seleka a Afrika ta Tsakiya
'Yan tawayen Anti-Balaka da ke fada da na Seleka a Afrika ta Tsakiya AFP / Andoni Lubaki
Talla

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Afrika ta Tsakiya, Aurelien Agbenonci ya bayyana cewa an kai harin ne a Ngakobo mai nisan kilomita 60 daga garin Bambari wanda ke yankin kudancin kasar.

Shi kuwa mataimakin mai magana da yawun sakatare Janar na Majalisar Farhan Haq ya yi karin bayani ne game da lamarin, inda ya ce an kashe mutane biyar daga cikin ‘yan tawayen na Seleka da yawancinsu Musulmai ne .

A ranar litinin din da ta gabata ne, Paparoma Francis ya ziyarci wani masallaci a babban birnin Bangui na kasar, inda ya bukaci Musulmai da Kristoci da su kawo karshen takun sakan da ke tsakaninsu wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban muatane a shekaru uku da suka gabata, lamarin da ya haifar da rarrabuwan kai a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.