Zaben shugabancin kasar Rwanda
A ranar juma’a ake gudanar da zaben shugaban kasa a Rwanda inda Paul Kagame wanda ya shafe tsawon shekaru 17 kan karagar mulki ya sake tsayawa takara.
Wallafawa ranar:
Shugaba Kagame ya taka rawa wajen inganta tattalin arzikin kasar, amma ana sukar lamirinsa saboda tsarinsa da wasu ke kallo a matsayin muzguna wa ‘yan adawa da kuma takaita fadin albarkacin baki.
A wannan alhamis ‘yan asalin kasar da ke zaune a waje sama da dubu 44 ne ke jafa nasu kuri’un domin zaben shugaba a wannan kasa da ta yi fama da rikicin kabilanci da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 800 a shekarar 1994.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu