Isa ga babban shafi
Rwanda

Sweden ta daure dan kasarta saboda Rwanda

Kotun kasar Sweden ta yanke wa wani mutum mai shekaru 61 hukuncin daurin rai da rai saboda samun sa da hannu a kisan kare dangi da aka yi a Rwanda a shekara ta 1994.

Kasusuwan mutanen da suka rasa rayukansu a tarzomar Rwanda
Kasusuwan mutanen da suka rasa rayukansu a tarzomar Rwanda © REUTERS/Finbarr O'Reilly
Talla

Kotun na birnin Stockholm ta ce, ta dauki matakin ne akan Claver Berinkindi a karkashin dokokin kasa da kasa saboda samun sa da laifin kisa da sace mutane a lokacin rikicin na Rwanda.

Mutumin dai dan asalin Sweden ne amma yana da tushe a Rwanda, yayin da kotun ta ce ya taka rawa a kisan kiyashin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu 800.

Dokar Swede ta bai wa kotu damar yanke hukunci ga dan kasar da kuma bako daga wata kasa daya aikata laifi, kuma a shekara ta 2007 ne kotun Rwanda mai suna Gacaca ta yanke ma sa hukunci a bayan idonsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.