Isa ga babban shafi
Tanzania

An ceto mahaka zinare 15 bayan share kwanaki 32 a gargashin kasa.

A kasar Tanzaniya an ceto mahaka ma’adanai 15 da rai bayan share tsawon kwanaki 32 makale a wata rijiyar hakar Zinare mai zurfin mita 35 da ta fada.

wasu mahaka zinare a kasar janhuriyar demokradiyar Kongo a yankin Ituri a  2006.
wasu mahaka zinare a kasar janhuriyar demokradiyar Kongo a yankin Ituri a 2006. AFP PHOTO / JOSE CENDON
Talla

Shaidun gani da ido tare da kafofin yada labaran yankin sun tabbatar da ceto mutanen da rai, kamar yadda Elias Makundi wani da ya halarci aikin ceton , ya sanar da kamfanin dillancin labaran Afp, cewa babu wanda ya rasa ransa a cikin mahakan sai dai wasu sun galabaita galabaita sosai.

Kafofin yada labarai dais un ce mahaka ma’adinan goma sha biyar da aka ceto, sun hada ne da yan kasar ta Tanzania 14 masu kimanin shekaru 19 zuwa 33 a duniya, sai kuma wani dan China guda, dukkansu kuma, sun tsira da rai a cewar majiyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.