Ana zargin wasu mutane biyar da kashe matukin jirgin Britaniya a Tanzania
Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ne ya bayar da umarnin kama wasu yan kasar biyar bisa laifin kakkabo helikoptar dan kasar Britaniyan a yayin da yake kokarin hana su cire hauren giwaye da aka kashe a gidan namun dajin Maswa dake arewacin kasar
Wallafawa ranar:
Matukin jirgin helikoptar mai suna Roger Gower yana da shekaru 37 kuma ya gamu da ajalinsa ne a yayin da yake kokarin hana wadanan mutanen masu fataucin hauren giwa da suka kewaye wasu gawarwakin giwaye a wani yankin gidan ajiye namun daji mai suna Maswa a arewacin kasar daga cire hauren giwayen.
Gower dai ya dadde yana aikin kare namun daji a Tanzania inda yake adawa da fataucin hauren giwa a wani mataki na ganin ba’a karas da wannan rukunin na dabbobi daga doron kasa ba.
Shugaba Magufuli ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici inda ya kuma sha alwashin hukunta duk wani wanda aka samu da hannu a kisan Mr Roger Gower, kwararru dai na ci gaba da gargadin kaucewa gushewar Giwaye daga doron kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu