Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Ana ci gaba da kashe giwaye a Zimbabwe

A kasar Zimbabwe jami’an dake kula da kare gandun daji sun gano gawawakin giwaye 26 .Ana zargin masu farautar hauren giwaye da yi amfani da guba wajen halaka wadanan namun daji.  

Wasu daga cikin giwaye a kasar Zimbabwe
Wasu daga cikin giwaye a kasar Zimbabwe Tanzania Govt
Talla

Hukumomin kasar sun bayyana cewa za su kadammar da bicinke a kai ,yanzu haka kungiyoyi da dama ne a kasar dama waje suka bayar da goyan baya zuwa hukumomin wannan kasa ta Zimbabwe domin ganin an kiyaye dama kare gandun daji a kasar.

Wata kungiyar kare namun daji da ake kira Space for Giant a Turance ta samar da wata fasaha da zata kare rayyukan Giwaye da ke rayuwa a dajin Laikipia a kasar Kenya. Akwai wata damara ta na’urar GPS da aka daurawa Giwayen domin sanin halin da suke ciki tare da yada rayuwarsu a dandalin Twitter.

Kungiyar Space for Giant kungiya ce da ke hada muhawara a dandaleyen zumunta kuma yanzu kungiyar ta fara yada yadda Giwaye ke rayuwa a dajin Laikipia a kasar Kenya.

Kungiyar tace wannan wani mataki ne na sanar da duniya irin yadda Giwaye ke rayuwa da kuma yadda suke mu’amula a muhallinsu.

Akwai dai Jami’ar da ke kula da yada rayuwar giwayen a shafin Twitter daga Birtaniya wanda wani da ke kula da rayuwar Giwayen ke aikawa da bayanai daga Kenya a cikin dakikoki.

Kungiyar tace ta dauki wannan matakin ne domin kare rayukan giwayen da ake kashewa domin yin tsafe-tsafe ko samar da magani.

Kasashen Kenya da  Zimbabwe na daga cikin kasashe a Duniya dake da albarkatun gandun daji.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.