Sojojin Tanzania sun yi wa mata Ciki a Congo
Majalisar Dinkin Duniya tace wasu ‘yan mata 11 daga Jamhuriyar Demokiradiyar Congo sun ce sojojin samar da zaman lafiya daga kasar Tanzania sun musu ciki. Kakakin Majalisar Farhan Haq yace 7 daga cikin matan har sun haihu, kuma 6 daga cikin su kananan yara ne.
Wallafawa ranar:
Jakadan Tanzania a Majalisar Dinkin Duniay ya ce zasu tura tawagar masu bincike Congo don tabbatar da gaskiyar zargin.
Sojojin Tanzania dai na cikin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da aka tura aikin wanzar da zaman lafiya a Mavivi lardin gabashin Arewavin Kivu mai fama da rikici a Jamhuriyyar Congo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu