Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

An sake zargin dakarun MDD da yin lalata a Afrika ta tsakiya

A Karo na 17 an sake samun zargin fyade da ake yi wa sojojin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin samar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya à Bangui.
Sojojin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya à Bangui. AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Ana zargin Dakarun ne da yin lalata da yara kanana.

Shugaban aikin samar da zaman lafiya na Majalisar Herve Ladsous ya bayyana zargin a matsayin abin da ke tayar da hankali lokacin da ya ziyarci kasar a jiya Talata.

Jami’in ya ce daga cikin zarge zarge 17, 13 daga cikinsu ana yi wa sojoji ne, daya kuma ana yi wa Dan sanda, biyu ana yi wa fararen hular da ke yi wa Majalisar aiki.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta hanzarta hukunta sojojin da aka gano suna da hannu wajen yin lalata da yara kanana a Jamhuriyar Afrikaa ta tsakiya.

Tuni dai aka tube Babban Jekadan Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Babacar Gaye sakamakon batun yin lalata da mata da ake zargin dakarun Majalisar da aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.