Isa ga babban shafi
Mali

An kashe dakarun MDD a Mali

Hukumomin majalisar dinkin dniya sun bayyana cewa, dakarun majalisar guda 6 da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali, na cikin sojoji guda 9 da mayakan Ansaroudine suka hallaka bayan sun kai farmaki a sansanin soji da ke arewacin kasar a jiya jumma'a.

Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon ya yi alla-wadai da harin.
Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon ya yi alla-wadai da harin. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Sakatetare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya yi Allah-wadai da harin wanda ya raunana sojoji 30 yayin da wata majiya ke cewa, sojojin da mayakan suka kashe ‘yan asalin kasar Guinea ne.

Rahotanni sun ce wata mota ce dauke da ‘yan kunar bakin wake ta ratsa cikin sansanin sojin da ke Kidal bayan mayakan jihadin sun harba Roka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.